Monday, February 17, 2020

kalubale gareku iyan-matan zamani:


kalubale gareku iyan-matan zamani:
from my facebook  account.

kasancewar ba komai ne nake magana akan shi ba, so dayawa nakan dauki lokaci banyi magana akan komai ba, sai in bukatar hakan ta kama.kuma Hakika har Awurin Allah inayin wadannan rubuce-rubucen ne domin kawai "AL'AMRU BIL MA'ARUF WAN NAHYU ANIL MUNKAR" kusan shine babban dalilin zamana acikin wannan kafar sadarwa ta facebook.
Annabi s.a.w acikin hadisi ingantacce acikin muslim yake cewa"duk wanda yaga wani abin ki to ya gusardashi da hannunshi, idan bazai iya ba to yayi da bakinsa, idan bai samu iko ba, to (ya kyamaci abin) acikin zuciyarsa, kuma wannan shine mafi raunin imani"
A dalilin wannan hadisin yazama wajibi ga duk wani musulmi idan yaga wani abu na barna na faruwa to yayi kokarin chanza shi da gwargwadon yanda ya samu iko. sanin kowane a wannan lokaci  iyan-mata da yawa musamman iyayan musulmai sun shiga wani yanayi! wannan yanayin shine tsiraici da shigar banza ta zama bakomai ba awajensu, kadubi yanda iyayan musulmai musamman a makarantun mu na boko kai harma da islamiyyu: yanda wadannan iyan-matan suke  shiga irin wadda bata dace da musulunci ba , islamiyya  yarinya zata tafi amma sai kaga tayi kwalliya harda make-up da sanya turare ! wannan wane irin lalacewar tarbiyane, inda ma abun yafi tsanani shine idan kashiga acikin manyan makarantu na gaba da sakandire zakaga shiga iri-iri, wai kuma suna ganin wannan shine wayewa, musamman iyayan hausawa(hausa/fulani),  kuma sai kaga suna yima sauran mata wadanda basa wannan shigar ta tsiraici:dubin kauyawa wadanda basu wayeba, wa-iyazubillahi!!! to ku sani wannan ba dabi’ar kwarai bace, kuma wadannan matan(sisters) da kuke renawa wai don suna sanya hijabi da niqabi, kusani sunfiku qima ko a wajen jama’a, idan harku kuna yimusu dubin wai ai ba hausa/Fulani bane! Har kuna cewa ai yarbawane , ai inyamuraine! Duk yaushe suka musulunta, to sai muce muku  badai sun musulunta ba, ai shikenan ba ruwanmu da kabilunsu.ya kamata kudawo cikin hankalinku, kusani wannan abun sabon Allah ne,zunubi ne kuke samu, domin Annabi ya hana mace ta fita tasanya turare, har ya nuna idan mace ta fita ta sanya turare to mazinaciya ce, Amma a yanzu mafi yawan mata basu damu da wannan hadisin ba, sunayin kwalliyar sune yanda suka ga dama, suna ta samun tsinuwa daga mala’iku da mutane!!!
To kudawo cikin hankalinku, kusani mutuncinku shine Sanya hijabi da lullubi kamar yanda aka san matan musulmai, kuma mafi abinda yafi mutunci a gareku shine yin aure, rashin auren duk shike kawo wadannan fitintinun,..
A saboda haka ina kiraga iyaye su sani iyayansu kiwo ne Allah ya basu, kuma haqiqa zai tambayesu akan wannan kiwon da yabasu, suyi iya kokarinsu wajen tarbiyantar da iyayansu musamman mata, a, rinka umurtarsu da sanya hijabi aduk inda zasuje, malamai na islamiyya kalubale gareku kuma ku kula sosai, kuma yanne maza kurinka kula yanda tasarrufin kannenku mata yake gudana domin samun saukin wannan al’amarin, dukkanmu munsani wadannan irin sabon Allah da tsiraici shike haifarda zina, ita kuma zina itake kawo fushin Allah, to saboda haka sai mun tashi tsaye munyaki wannan fitina,,
Dafatar Allah ya shiryardamu baki daya,…
daga Abdullahi ahmad jimajimi,  

No comments:

Post a Comment