kalubale gareku iyan-matan zamani:
from my facebook account.
kasancewar ba komai ne nake magana akan shi ba, so dayawa
nakan dauki lokaci banyi magana akan komai ba, sai in bukatar hakan ta
kama.kuma Hakika har Awurin Allah inayin wadannan rubuce-rubucen ne domin kawai
"AL'AMRU BIL MA'ARUF WAN NAHYU ANIL MUNKAR" kusan shine babban
dalilin zamana acikin wannan kafar sadarwa ta facebook.
Annabi s.a.w acikin hadisi ingantacce acikin muslim yake
cewa"duk wanda yaga wani abin ki to ya gusardashi da hannunshi, idan bazai
iya ba to yayi da bakinsa, idan bai samu iko ba, to (ya kyamaci abin) acikin
zuciyarsa, kuma wannan shine mafi raunin imani"
A dalilin wannan hadisin yazama wajibi ga duk wani musulmi
idan yaga wani abu na barna na faruwa to yayi kokarin chanza shi da gwargwadon
yanda ya samu iko. sanin kowane a wannan lokaci
iyan-mata da yawa musamman iyayan musulmai sun shiga wani yanayi! wannan
yanayin shine tsiraici da shigar banza ta zama bakomai ba awajensu, kadubi
yanda iyayan musulmai musamman a makarantun mu na boko kai harma da islamiyyu:
yanda wadannan iyan-matan suke shiga
irin wadda bata dace da musulunci ba , islamiyya yarinya zata tafi amma sai kaga tayi kwalliya
harda make-up da sanya turare ! wannan wane irin lalacewar tarbiyane, inda ma
abun yafi tsanani shine idan kashiga acikin manyan makarantu na gaba da
sakandire zakaga shiga iri-iri, wai kuma suna ganin wannan shine wayewa,
musamman iyayan hausawa(hausa/fulani),
kuma sai kaga suna yima sauran mata wadanda basa wannan shigar ta
tsiraici:dubin kauyawa wadanda basu wayeba, wa-iyazubillahi!!! to ku sani
wannan ba dabi’ar kwarai bace, kuma wadannan matan(sisters) da kuke renawa wai
don suna sanya hijabi da niqabi, kusani sunfiku qima ko a wajen jama’a, idan
harku kuna yimusu dubin wai ai ba hausa/Fulani bane! Har kuna cewa ai yarbawane
, ai inyamuraine! Duk yaushe suka musulunta, to sai muce muku badai sun musulunta ba, ai shikenan ba
ruwanmu da kabilunsu.ya kamata kudawo cikin hankalinku, kusani wannan abun
sabon Allah ne,zunubi ne kuke samu, domin Annabi ya hana mace ta fita tasanya
turare, har ya nuna idan mace ta fita ta sanya turare to mazinaciya ce, Amma a
yanzu mafi yawan mata basu damu da wannan hadisin ba, sunayin kwalliyar sune
yanda suka ga dama, suna ta samun tsinuwa daga mala’iku da mutane!!!
To kudawo cikin hankalinku, kusani mutuncinku shine Sanya
hijabi da lullubi kamar yanda aka san matan musulmai, kuma mafi abinda yafi
mutunci a gareku shine yin aure, rashin auren duk shike kawo wadannan
fitintinun,..
A saboda haka ina kiraga iyaye su sani iyayansu kiwo ne
Allah ya basu, kuma haqiqa zai tambayesu akan wannan kiwon da yabasu, suyi iya
kokarinsu wajen tarbiyantar da iyayansu musamman mata, a, rinka umurtarsu da
sanya hijabi aduk inda zasuje, malamai na islamiyya kalubale gareku kuma ku
kula sosai, kuma yanne maza kurinka kula yanda tasarrufin kannenku mata yake
gudana domin samun saukin wannan al’amarin, dukkanmu munsani wadannan irin
sabon Allah da tsiraici shike haifarda zina, ita kuma zina itake kawo fushin
Allah, to saboda haka sai mun tashi tsaye munyaki wannan fitina,,
Dafatar Allah ya shiryardamu baki daya,…
daga Abdullahi ahmad jimajimi,